Rahotanni daga jihar Filato na cewa Kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige Hon Moses Sule, kakakin majalisar dokokin jihar.
Daily trust ta ruwaito cewa an tsige kakakin majalisar, dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da Danjuma Azi, dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta arewa maso yamma a majalisar dokokin jihar.
Kotun ta ayyana tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Naanlong Daniel da Hon. Mark Na’ah, dukkansu yan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wadanda suka lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.
Wadanda suke kara sun kalubalanci daukar nauyin Sule da Azi kan hujjar cewa PDP bata cancanci shiga zaben ba saboda jam'iyyar bata da tsari.
Published by isyaku.com