Kwankwaso ya shiga sabon matsala, uwar jam'iyar NNPP ta amince da korarsa daga jam'iyar



Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da rushe kwamitin ayyuka na NWC karkashin jagorancin Abba Kawu Ali. Legit Hausa ya wallafa.

Kwamitin BoT ta kuma tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwakwanso, rahoton Nigerian Tribune.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron BoT na jam’iyyar NNPP wanda ya gudana a Otal din Rockview da ke Apapa, jihar Lagas a ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba.

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar na 2022 zai ci gaba da kasance yadda yake cewa ba za a yi la'akari da gyara shi ba har sai bayan babban zaben 2027.

Sakataren labaran jam'iyyar na kasa, Alhaji Abdulsalam Abdulrasaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka gabatarwa manema labarai.

Published by isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN