Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) da ke Operation Hakorin Damisa IV sun gano wata masana’antar kera bindigogi a Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna tare da cafke wani mai kera bindigogi da ake nema ruwa a jallo.
Rundunar sojin Najeriya a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 22 ga watan Satumba, 2023, ta ce gano masana’antar ya biyo bayan samamen da jami’an leken asiri suka yi na tsawon mako guda wanda a karshe ya kai ga cafke dan bindigan mai suna Napoleon John.
A cewar sanarwar, wanda ake zargin wanda ya amsa laifin da ake zargin ya aikata, ya jagoranci sojoji zuwa masana’antar da aka boye inda aka siyar da makamai daban-daban da wani bata gari mai suna Monday Dunia.
Published by isyaku.com