Gwamna ya fusata, ya bayar da kukuicin N100m ga duk wanda ya bada bayanin kan wadanda suka kashe DPO suka yi gunduwa-gunduwa da jikinsa


Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ba da umarnin dakatar da wani sarki har sai babata gani dangane da kisan gillar da ‘yan iska suka yi wa jami’in ‘yan sanda na Ahoada, SP Bako Angbashim, da “gungun masu laifi.”


 A baya dai LIB ta ruwaito cewa an kashe Bako ne a yankin Odiemudie da ke karamar hukumar Ahoada ta Gabas (LGA) a jihar a yayin wani artabu da wasu ‘yan kungiyar asiri a yankin. 


 A wata sanarwa da da kansa ya sanya wa hannu, gwamnan ya bayyana bakin cikinsa kan kashe dan sandan.  Gwamna Fubara ya lura cewa manyan wadanda ake zargin, “Mr.  Gift David Okpara Okpolowu (aka 2-Baba) da dukkan mambobin kungiyar sa masu aikata laifuka”, an bayyana neman su nan take.  Ya kuma sanar da bayar da tukuicin N100,000,000 ga duk wanda ya samu bayanai masu amfani da ya kai ga kama Okpolowu da gurfanar da shi gaban kuliya.


 Ya kara da cewa an dakatar da Mai Martaba, Basarake Eze Cassidy Ikegbidi Eze Igbu Akoh II, har sai baba ta gani, saboda laifin da ya yi na bai wa David Gift da ‘yan kungiyarsa damar gudanar da ayyukansu cikin walwala, tare da gudanar da ayyukansu na laifuka a yankin da yake da iko.”


Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN