Wata dalibar jami’ar jihar Gombe da ke Gombe ta shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin kashe jaririyarta mai kwana daya da haihuwa wanda ta jefar daga hawa na biyu na dakin kwanan dalibai mata.
An tsinci gawar jaririn ne da sanyin safiyar ranar Asabar 9 ga watan Satumba a kusa da Hall IV na dakunan kwanan dalibai mata. Wani dalibi da ke wucewa ya gan jaririn, ya gano cewa jaririn ya riga ya mutu sakamakon rauni da ya samu a kafarsa ta dama. LIB ta rahoto.
Wata dalibar makarantar ta ce mahaifiyar jaririn ta shafe watanni tana boye ciki a cikin rigar hijabi don kada a gano tana da ciki.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na Jami’ar, Mohammed Abubakar, ya ce;
“An tabbatar da cewa an jefar da jariri daga hawa na daya daga cikin gidajen kwanan dalibai mata, wannan babban laifi ne kuma jami’a na bincike kuma za a dauki matakin ladabtarwa a kansa saboda laifi ne a kashe jariri. Idan har maganar haihuwa ce a yanzu babu matsala, amma jefar da jaririn da ba shi da laifi ya mutu, wannan laifi ne,” inji Abubakar.
Kalli bidiyon yadda dalibar macen aka raka ta zuwa ofishin 'yan sanda a kasa…
Published by isyaku.com