Wasu ’yan uwa biyu suna tsare a ofishin ‘yan sanda na Tudun Wada da ke garin Gusau a Jihar Zamfara, bisa zargin kashe wani wakilin Muryar Najeriya, Hamisu Danjigba.
Wadanda ake zargin, Bilal Haruna da, Mansur Haruna, ‘ya’yan yayan marigayi Danjigba ne, Malam Haruna.
Suna zaune ne a gidan marigayi Danjigba da ke unguwar Samaru a birnin Gusau, kafin kisan.
Danjigba, wanda aka bayyana bacewarsa a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, ya koka a lokuta da dama kan rashin da'a na mutanen biyu, wadanda 'yan uwansa ne.
Bayan ya bace ne aka aika da sako ga iyalansa. A sakon text na wayar salula, wanda ya aika ya bukaci N1m a matsayin wani bangare kafin a bayyana kudin fansa na karshe ranar Juma'a.
Abin baƙin ciki, an tsinci gawarsa a ranar Laraba, 20 ga Satumba, an jefar da shi a wani laka a bayan gidansa.
An kama ‘yan uwansa dangane da kisan nasa, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Danjigba yayi aiki a gidajen yada labarai da dama kamar, Jaridar Ayau, Kunnen Gari, Muryar Najeriya da FM Nigeria.
Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki.
Published by isyaku.com