Kotun sauraron kararrakin zabe ta kasa da ta jiha da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato, ta tsige wasu ‘yan majalisar jam’iyyar PDP uku.
Wadanda aka tsige sun hada da Remvyat Nanbol, Agbalak Adukuchill da Happiness Akawu, masu wakiltar Langtang ta tsakiya, Rukuba/Iregwe da Pengana a majalisar dokokin jihar. Daily trust ta ruwaito.
An yanke hukuncin ne a jajibirin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Dr. Nentawe Yiltwatda, dan takarar jam’iyyar APC a zaben, yana kalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya tsaya takara a karkashin PDP.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 525,299 inda ya doke Yiltwatda wanda ya samu kuri’u 481,370, amma dan takarar jam’iyyar APC ya garzaya kotu.
A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, kotun ta bayyana Daniel Ninbol Listic na jam’iyyar Labour (LP), Bako Ankala da Yakubu Sanda na APC wadanda suka zama na biyu a zaben a matsayin wadanda suka yi nasara.
Da yake yanke hukunci, kwamitin da Mai Shari’a Muhammad Tukur ya jagoranta, ya ce ‘yan majalisar da aka tsige ba su da wata ka’ida ta daukar nauyin jam’iyyar PDP duba da yadda suka ki bin umarnin kotu na gudanar da taron gundumomi da zai ba su damar samun ingantaccen tsari.
Ya kara da cewa PDP ba ta da tsari don haka ba za ta iya daukar nauyin ‘yan takarar zabe ba.
Kotun ta kuma bayyana cewa masu shigar da kara suna da hurumin kalubalantar shiga ko shigar da PDP a zaben.
Shugaban kotun ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe daga korarrun ‘yan majalisar tare da bayar da sabbi ga wadanda suka lashe zaben.
Daily trust ta rawaito cewa kotun ta tsige wasu ‘yan majalisar dokokin jam’iyyar PDP guda hudu da suka hada da Sanata saboda tsarin jam’iyyar.
Published by isyaku.com