Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da suka kashe wani ma’aikacin POS mai suna Olasunkanmi Joseph tare da kwashe masa kudi N3.5m a Ado-Ekiti.
Ku tuna cewa an kashe Olasunkanmi a Irona Roundabout da ke Ado Ekiti da rana tsaka a ranar Alhamis, 6 ga Afrilu, 2023, yayin da yake dawowa daga banki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya ce an kama wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne bayan da aka samu labarin cewa suna shirin sake kai wani harin fashi da makami daga maboyar su.
Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na kasancewa mambobin kungiyar asiri ta Supreme Eiye Confraternity a Ikere-Ekiti kuma suna da hannu wajen kai hare-hare na fashi da kuma garkuwa da mutane.
A cewar PPRO, bindigar AK-47 da aka samu daga hannun wadanda ake zargin na daga cikin makaman da aka yi amfani da su wajen kashe ma’aikacin POS.