Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe wasu dalibai uku na kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai l da ke garin Lafiya a jihar Nasarawa. Daily trust ta rahoto.
An tattaro cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wata daliba guda daya da aka bayyana sunanta da Ajoke, dalibar ND ll a fannin fasahar kimiyya.
Daily trust ta gano cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 08:00 na daren ranar Litinin.
Daliban da suka samu raunuka harbin bindiga, an ce suna karbar magani a asibiti.
Published by isyaku.com