Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da Maulidin Manzon Allah (SAW).
A cikin wata sanarwa da babban sakatare, Dr Oluwatoyin Akinlade, ya fitar a madadinsa, Ministan harkokin cikin gida, Hon Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar ta bana. Ya kuma gargade su da su zama ruhin soyayya da hakuri da juriya, wadanda su ne zurfafan dabi’u na ruhi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya misalta.
Ministan ya bukaci matasa su rungumi aiki tukuru da zaman lafiya ga ’yan kasa ba tare da la’akari da imani, akida, da kabilanci ba.
Published by isyaku.com