Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta gargadi mazauna yankin da su guji yada labaran karya game da bacewar al'aurar maza a yankin.
Rundunar ta ba da wannan gargadin ne bayan da wasu fusatattun mutane suka kashe wani mutumi da har yanzu ba a tantance ko wanene ba, wanda ake zargi da satar al'aurar wani matashi a karamar hukumar Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja.
LIB ta rahoto cewa a baya ma wani mutum ya tsera bayan an kama shi aka lakada mashi duka bisa zargin satar al'aurar wani mutum a Gwagwalada.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya, SP Josephine Adeh a wata sanarwa da ta fitar, ta ce kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna Garba, ya yi gargadin cewa irin wannan jita-jita na iya haifar da fargabar jama’a da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.
“Wani al’amari da ya shafi Rokeeb Saheed, wanda ya zargi Lucky Josiah da haddasa bacewar al'aurarsa, ya jawo wannan gargadin. Bayan an duba lafiyar sa, an tabbatar da cewa al'aura Saheed na nan daram, bayan an ci zarafin Josiah,” in ji sanarwar.
A wani lamari makamancin haka, biyo bayan ikirari da wani baligi, wanda ba a san sunansa ba ya yi, wasu Fusatattun matasa su yi wa wani mai suna John Ugwu 'm' mai shekaru 17 dukan tsiya a ranar 21/09/2023 da misalin karfe 1940. a phase 2 Gwagwalada
“Jami’an ’yan sandan da ke hedikwatar ’yan sanda reshen Gwagwalada suka yi gaggawar zuwa wurin, inda suka yi nasarar ceto shi, suka garzaya da wannan balagaggen zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon mummunan raunuka da aka yi masa bisa zargin wani mutum, kuma zargin karya,” in ji PPRO.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Haruna G. Garba, ya yi gargadin daukar tsauraran matakai kan yada labaran karya, ya kuma bukaci jama’a da kada su dinga yin hukuncin Yan daba. Rundunar ‘yan sandan FCT ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro”.