Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da 'yanci (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya binciki $15bn da N200bn da suka bata a kudaden shiga na man fetur. Channels TV ta rahoto.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, mataimakin daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya bukaci Tinubu ya “ kafa kwamitin bincike na fadar shugaban kasa don gaggauta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi cewa sama da dala biliyan 15 da aka samu na kudaden man fetur, da kuma Naira biliyan 200 da aka ware domin gyara matatu sun bace kuma ba wani bayani a kan su. Tsakanin 2020 zuwa 2021, kamar yadda Hukumar Kula da Masana'antu ta Najeriya (NEITI) ta tsara."
Oluwadare ya bukaci shugaban kasa da ya ba da sunan duk wanda ake zargi da hannu a bacewar kudaden da kuma tabbatar da gurfanar da su a gaban kotu tare da kwato duk wani abin da aka samu na aikata laifuka.
“Akwai halaltacciyar maslahar jama’a wajen tabbatar da adalci da bin diddigin wadannan manyan zarge-zarge. Daukar wadannan muhimman matakan zai kawo karshen rashin hukunta masu laifi,” in ji sanarwar.
“A matsayinka na Shugaban kasa kuma Ministan Albarkatun Man Fetur, ya kamata ofishinka ya damu da wadannan munanan bayanan, ta hanyar yin la’akari da zarge-zargen da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin nan take, kuma an kwato duk wasu kudaden jama’a da suka bace.
Published by isyaku.com