Bayan hatsabibin kwarto ya kutsa gidan matar aure da safe kiri-kiri, ala dole ya gudu ya bar waya da silifas dinsa a dakin matar

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani Godstime Ekanem da ake zargi da shiga gidan auren wata mata mai suna Misis Jelila Oyinbo tare da yunkurin yi mata fyade.

 Kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 28 ga Satumba, 2023, ya ce lamarin ya faru ne a Mowe-Ofada, karamar hukumar Obafemi Owode ta jihar.

 A cewar PPRO, matar ta ce Ekanem yana yi mata zancen banza na neman lalata da ita duk da gargadin da ta sha yi masa na ya rabu da ita saboda ita matar aure ce.

 Sai dai wanda ake zargin ya dage, kuma a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, ya shiga gidan matar ne a lokacin da mijinta ya fita.

 “Yau 28 ga watan Satumba, 2023 wata Misis Jelila Oyinbo “F” ta kamfanin MTN Estate a Mowe Ofada Jihar Ogun ta ruwaito cewa Godstime Ekanem ya yi ta takura rayuwarta na neman ya yi lalata da ita duk da ta yi masa gargadi cewa ita matar aure ce, amma Ekanem ya ki bari, ya tsaya tsayin daka kuma ya ci gaba da takura mata," in ji sanarwar.

 “A ranar 26 ga watan Satumba, 2023 da misalin karfe 0800 na safe, ya fahimci mijin nata ya bar gida, sai Ekanem ya shiga gidan aurenta ya kai mata hari da nufin ya yi lalata da ita.

 “Ta yi ta kokawa da shi inda ta sanar da surikinta Michael Oyewole wanda ya garzaya gidan don ceto Jelila, yayin da Ekanem ya boye kansa.

 Micheal ya yi fafatawa da Ekanem a cikin dakin inda ya kwada mashi guduma a kai,  Michael ya rama ta hanyar sare Ekanem da adda a kai'.

 “Ekanem ya gudu ya bar wayarsa da silifas a dakin matar.

 "'Yan sanda sun kama Ekanem yayin da aka kai Micheal Oyewole asibiti domin kula da lafiyarsa."

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN