Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki kauyen Kwarikwarasa da ke karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi a karshen makon da ya gabata, sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutanen kauyen su bakwai.
Daily trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun mamaye al’ummar ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 9 ga watan Satumba.
Gwamna Nasiru Idris ya ziyarci al’umma inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi matakan dakile sake afkuwar lamarin. Ya ce ya bai wa jami’an tsaro dukkan goyon baya da hadin kan da ya kamata domin yakar miyagun ayyuka a fadin jihar.
Published by isyaku.com