Ya shaidawa kotun cewa matar ta sa ta dade tana faɗa ma sa cewa za ta yi ma sa kaciya, inda a yanzu haka ma ya ce ta sayo wuƙa mai kaifi don cika aniyarta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mijin, wanda ya kasance mata biyu gareshi, ya bayyana cewa tun ranar da ta yi wannan iƙirarin ya daina barci da idanu biyu a duk lokacin da zai kwana gidanta.
Alƙalin da ke kula da koken da aka shigar Malam Sunusi Danbaba Daurawa, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ɗage sauraron ƙarar, mijin ya bayyana cewa yanzu haka dai ya yi nasarar ɗauke wukar daga ɗakin matar ta sa, sai dai har yanzu hankalinsa bai kwanta ba.
Malam Ali ya kuma bayyana cewa bai san dalilin da ya sa matar ta sa ta yi hakan ba, saboda a cewarsa suna zaune lami-lafiya da ita.
Ya ƙara da cewa yana matuƙar ƙaunar matarsa, amma kuma ga abinda take shirin aikatawa, wanda ya sanyi shi kawo ƙararta gaban kuliya domin a tsayar da ita.
Manema labarai da suka yi kokarin jin ta bakin wannan mata kan abinda take shirin aikatawa, taki yadda ta yi hira da su.
Published by isyaku.com