Miyagu sun kama DPO na Yan sanda sun yi gunduwa-gunduwa da gawarsa bayan sun sheke shi a jihar kudu


Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Satumba, sun harbe jami’in ‘yan sandan shiyya ta Ahoada (DPO) a jihar Ribas, SP Bako Angbashim.


 Rahotanni sun bayyana cewa, SP Bako da mutanensa sun yi artabu da wani kasurgumin shugaban kungiyar asiri a yankin mai suna 2baba, inda harsashi ya kare masu.  Sai dai kuma ba su samu wani agaji daga Yan sanda ba, sakamakon haka Yan sandan suja ja da baya, amma abin takaici, ‘yan kungiyar asiri sun kama DPO da ya samu raunukan harsashi a lokacin musayar wuta, yayin da wani dan sanda da ya samu rauni ke jinya a wani wuri da ba a bayyana ba.


 A wani faifan bidiyo mai ban tsoro da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne suka fitar, an gan gawar Mista Bako an yi gunduwa-gunduwa da ita, yayin da aka ji wata murya tana masa ba’a.


 SP Bako ya taba yin aiki a karamar hukumar Khana ta Ogoni inda ya shahara saboda kwazonsa na halartar bikin ba takalmi.


 Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta ce ‘yan sanda na kan bin diddigin wadanda ake zargin domin ganin sun kama su tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN