Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Bola Tinubu na tunanin bayar da tallafin danyen man fetur na wucin gadi yayin da farashin danyen mai da kuma farashin kudaden waje ke ci gaba da hauhawa.
Majiyoyin fadar shugaban kasa sun shaidawa TheCable cewa, shawarar tana kan teburi kuma “ainihin” adadin man fetur da ake sha a kasar yanzu an san shi bayan cire tallafin jim kadan bayan kaddamar da Tinubu. Ɗaya daga cikin majiyoyin sun lura cewa adadin da aka kashe akan tallafi "a yanzu ana iya sarrafa shi".
Hakan na zuwa ne bayan da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) Limited ya ce babu wani shiri na kara farashin man fetir duk da tashin farashin danyen mai, tsadar rayuwa, da faduwar darajar Naira.
Published by isyaku.com