FG ta janye tuhumar da ake yi wa Emefiele, ta kuma shigar da sabbin tuhume-tuhume har guda 20 a kansa


Gwamnatin tarayya ta janye tuhumar mallakar makami ba bisa ka’ida ba da ta shigar a gaban kotun tarayya da ke Legas a kan dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele
.


 Ku tuna cewa Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da belin Emefiele kan Naira miliyan 20 bayan an gurfanar da shi tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan yari na Ikoyi, har sai an cika sharuddan belinsa.


 Duk da cika sharuddan belin, hukumar DSS ta ci gaba da tsare Emefiele a gidan yari saboda wasu dalilai na bincike.


 A ranar Talata, 15 ga watan Agusta, Daraktan shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta tarayya, Mohammed Bakodo Abubakar, ya je babbar kotun tarayya da ke Ikoyi da bukatar baka ta janye tuhumar mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.


 Lauyan da ake kara, Joseph Daudu (SAN) ya nuna adawa da hakan, wanda ya zargi gwamnatin tarayya da kin bin umarnin kotun farko da ta bayar da belin Emefiele.


 Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala shari’ar, Abubakar ya ce an shigar da sabbin tuhume-tuhumen a babbar kotun birnin tarayya Abuja.  Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi Emefiele da "ba da fa'ida ba bisa ka'ida ba" watau conferring unlawful advantages”.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN