Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malamin addinin Islama, Malam Murtala tare da yin garkuwa da wasu mutane bakwai a garin Bungudu, hedikwatar karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun mamaye garin ne a safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2024, inda suka yi awon gaba da Abdurrahman Hassan, dan sarkin Bungudu na farko; Abubakar Sarkin-Fada, tsohon ma'aikacin gwamnati; Amina Salisu, matar aure; da wasu mata hudu.
An ce ‘yan ta’addan sun shiga garin kai tsaye bayan tsakar dare inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili, wani majiya mai suna Ibrahim Bungudu ya shaida wa Premium Times.
Published by isyaku.com