Yadda wani mutum ya bindige abokinsa har lahira garin gwada layar bindigaAn rahoto cewa wani mutum mai suna Bode ya gudu bayan ya kashe wani mai suna Tunde Akinmoyewa da bindiga kirar gida a kauyen Laoso da ke karamar hukumar Ondo ta Yamma a jihar. Wata majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa, abokin nasa ne ya harbe tsohon mai mai shekaru 27 a duniya yayin da yake gwada wata sabuwar bindiga da aka kera a cikin gida a ranar Talatar da ta gabata.  Majiyar ta ce; “Don gwada ingancin laya, Tunde ya nemi abokinsa (Bode) da ya fara harbe shi.  Bayan abokin Tunde ya dauko mutumin ya harbe shi (Tunde), kwatsam sai ya fadi ya mutu nan take.

 "Bayan ganin abin da ya faru, wanda ake zargin ya ranta a na kate kafin makwabta su isa wurin kuma ba a kama shi ba." An garzaya da marigayin asibiti mafi kusa da kauyen, inda aka tabbatar da rasuwarsa.  Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, Funmilayo Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin. Odunlami ta ce; “Wani tsohon mai laifi da ya taba zaman gidan yari mai suna Tunde Akinmoyewa, wanda kuma dan kungiyar asiri ne, a lokacin da yake gwada wata bindigar da aka kera a cikin gida da ake kyautata zaton an sayo shi, an bindige shi bisa kuskure daga cikin yaran sa mai suna Bode, wanda har yanzu ba a san sunan sa ba, sakamakon haka ya mutu".

 "A halin da ake ciki, an ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa yayin da ake kokarin kama wanda ake zargin."

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN