NYSC Ta Yi Martani Kan Tura Masu Bautar Kasa Nijar Don Taimaka Wa Sojoji A Yaki


Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don taimaka wa sojoji.


Daraktan hulda da jama'a na hukumar, Mista Eddy Megwa shi ya bayyana haka a ranar Asabar 5 ga watan Agusta a Abuja. Legit ya wallafa.


Sanarwar na zuwa ne bayan yada wani faifan bidiyo da aka yi a kafafen sada zumunta cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don yin yaki, PM News ta tattaro.


Ya ce:


"Hukumar NYSC na sanar da ku cewa babu kanshin gaskiya a bidiyon da wani mai barkwanci ke yadawa."
Megwa ya ba wa iyalan matasan da sauran mutane hakuri


Ya kara da cewa kamar yadda New Telegraph ta tattaro:



"Mutane da matasa masu bautar kasa da iyalansu duk su yi watsi da wannan labari da ke dauke da karairayi.


"Duk wasu masu barkwanci an shawarce su da su guji yada jita-jita da ke kawo cikas ga zaman lafiyar kasar."


Megwa ya ce hukumar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta kamo wadanda suka yada wannan labari don su girbi abinda su ka shuka, cewar Leadership.


Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN