Wata Soja ta bindige kyaftin din soja har lahira a Adamawa


Wata Soja da ke aiwatar da dokar hana fita da gwamnatin Adamawa ta sanya ta kashe wani babban abokin aikinta a wani shingen bincike a Yola, babban birnin jihar.


 Daily trust ta ruwaito cewa, matar sojan mai suna Lance Kofur Nkiru ta bindige wani kaftin din da ya yi kokarin shiga tsakani a rikicin da ta yi da jama’a a Round Service da ke babban birnin jihar.


 Shaidun gani da ido sun ce matar sojan ta dage cewa dole ne masu ababen hawa da ke dawowa gida a lokacin dokar hana fita.  Wasu daga cikinsu sun bayyana kansu a matsayin ma'aikata a kan muhimmin aiki amma ta tsaya tsayin daka.


 "Wasu mutane sun tsaya a wurin binciken sun bayyana kansu a matsayin ma'aikata a kan muhimman ayyuka amma sojan mace ta dage cewa dole ne su koma.  Wani kyaftin ne ya zo ya sa baki.  Sai dai abin takaicin ta riga ta harba bindigarta, don haka sai kawai ta harbe shi ta kashe shi bisa kuskure,” in ji wani jami’in tsaro.


 An ce an garzaya da wanda ake zargin zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yola, inda aka tabbatar da mutuwarsa, yayin da nan take sojoji suka kama wanda ake zargin suka tafi da ita.


 An dai sha zargin matar sojan da muzgunawa fararen hula, inda sau da yawa take dana kunamar bindigar kan karamin matsala.


 Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar ta-bacin ne bayan wasu ‘yan bindiga sun kutsa cikin ma’ajin gwamnati tare da wawashe kayayyaki da dama, ciki har da kayayyakin jin dadin rayuwa da nufin dakile tasirin radadin janye tallafin man fetur.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN