An sace babban sarkin ne a jiya Lahadi 6 ga watan Agusta da dare a fadarsa da ke garin tare da mai dakinsa a karamar hukumar Karu da ke jihar. Legit ya wallafa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel shi ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels a yau Litinin 7 ga watan Agusta.
Kakakin rundunar a jihar ya bayyana kara tura jam'ian tsaro yankin
Ya ce sun samu labarin sace sarkin ne a fadarsa da ke yankin Mararraba a cikin karamar hukumar Karu da ke jihar.
Rahman ya ce sun tura jami'an tsaro da 'yan kungiyar sa kai a cikin dazukan yankin don ceto sarkin da iyalinsa, Politics Nigeria ta tattaro.
Har ila yau, ya tabbatar da cewa ba a samu nasarar ceto wadanda aka sacen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
'Yan sanda sun bazama dazuka neman masu garkuwan
A kokarin ceto sarkin da iyalinsa, an kara tura jami'an 'yan sanda da kuma bangaren kwararru na hana garkuwa zuwa dazukan don kwato wadanda aka sacen, cewar Punch.
Jihar Nasarawa na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara da ke jihar.
A kwanan nan 'yan bindiga sun kai hari gidan tsohon minista Labaran Maku a lokacin mulkin Goodluck Jonathan tare da raunata mutunre da dama.
Published by isyaku.com