An kaddamar da bincike kan kisan wani babban jami'in 'yan sanda da karamin abokin aikinsa ya yi a karkashin wani yanayi da ba a tabbatar ba a yankin Nakuru na kasar Kenya.
Kwamandan ‘yan sandan karamar hukumar Nakuru Samuel Ndanyi ya tabbatar da cewa wanda ake zargi, dan sanda Jackson Ndonga ya harbe Christopher Kimeli har lahira a lokacin da yake a hedikwatar yankin K9 na Rift Valley da ke yankin Gabashin Nakuru a safiyar ranar Talata 8 ga watan Agusta.
Ndanyi ya ce;
"Mun samu rahoto da misalin karfe 5 na safe daga wani dan sanda da ya ji karar harbin bindiga a cikin Sashen Kare, a wurin da lamarin ya faru, mun gano cewa wani karamin abokin aikinsa ya harbe jami'insa daya har lahira."
Nan take aka kwance wa dan sandan makamai, kuma a halin yanzu yana tsare a babban ofishin ‘yan sanda na Nakuru. Ana hasashen cewa mai yiwuwa dan sandan ya harbe sajan ne saboda rashin jituwa da ke tsakaninsu. Rahoton 'yan sanda ya karanta;
"Har yanzu ba a tabbatar da manufar jami'in ba, duk da haka, abokan aikinsu sun yi hasashen cewa Jackson Konga da Christopher Kimeli basu jituwa."
Published by isyaku.com