Allah Sarki: Fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu 'Karkuzu' ya makance


Fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu ya makance a lokacin da yake fama da wata cuta.

 Jarumin wanda a yanzu yake neman taimakon kudi, yana fama da rashin lafiya tun watan Disambar 2020. Da yake zantawa da Daily trust, Karkuzu ya ce;

 “Yanzu ni makaho ne yayin da nake magana da ku.  Ina matukar bukatar taimakon kudi.  Ba ni da abincin da zan ci da ciyar da iyalina.

 “Gidan da nake zaune a ciki yanzu za a sayar da shi.  Idan sun sayar da wannan gidan, ban san inda zan dosa ba.  Don haka ne nake neman taimako daga ’yan Najeriya masu kishi da su kawo min agaji.  Aƙalla ƴan Najeriya su taimaka min siyan wannan gidan da nake zaune.

 “Na fuskanci tiyata  sau biyu, amma a karshe likitoci sun ce glaucoma ce, kuma ba zan sake gani ba.  Na yarda da hakan a matsayin makoma ta ta kaddara.  Amma ya kamata ’yan Najeriya su taimaka mini, su saya min gidan nan, da abinci.”

 Shuaibu ya fara fitowa a masana'antar nishadantarwa ta Hausa a shekarun 1980 tare da shahararriyar wasan kwaikwayo mai suna Karkuzu na Bodara wanda ya sanya ake masa lakabi da Karkuzu.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN