Nassara: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a Zamfara, Kebbi, Sokoto da Katsina, bayanai sun fito


Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) na shiyyar Arewa maso Yamma sun ci gaba da samun karin nasarori, yayin da suka kubutar da mutane 5 da aka yi garkuwa da su, tare da kashe ‘yan bindiga da dama, tare da kwato makamai da alburusai a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, da Katsina.


 Rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta, 2023, inda ta kara da cewa sojojin sun kuma kama wani da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke addabar gundumar Gigane da ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa, dakarun sojin Najeriya sun ci gaba da samun nassarori kan yan bindiga da barayin shanu da ke addaban jihohin, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Katsina tun lokacin da shugaba Bola Tinubu ya karbi mulki daga tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN