Wani matashi dan shekara 23 mai suna Abdulwahab Yusuf a ranar Talata, 8 ga watan Agusta, kotun shari’a ta jihar Kano ta tasa keyar shi zuwa gyaran hali, bayan ya amsa laifin satar fata (kpomo) da kudin sa ya kai N8,500. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Yusuf wanda ke zaune a Tukuntawa Quarters, Kano, an kama shi ne bayan mai shigar da kara, Fatihu Auwal wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Fagge, Kano, a ranar 5 ga watan Agusta.
Mai gabatar da kara, Insp Abdullahi Wada ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya shiga wurin wanda ya shigar da karar ya saci fatar saniya.
Bayan ya amsa laifin da ake tuhumar, Grand Khadi Umar Lawal-Abubakar ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 22 ga watan Agusta domin ci gaba da shari’a.
Published by isyaku.com