Wasu tsoffin ‘yan ta’addan Boko Haram sun gudanar da zanga-zanga a jihar Borno kan rashin biyansu alawus-alawus.
Tsoffin ‘yan ta’addan da ake tsare da su a sansanin Hajji da ke Borno bayan sun mika wuya ga gwamnatin Najeriya, sun haifar da cikas bayan tare babbar hanyar Bulumkutu zuwa Maiduguri a yayin zanga-zangar ranar Juma’a 18 ga watan Agusta.
Sun zargi gwamnatin tarayya da hana su alawus din N30k da aka yi musu alkawari.
Published by isyaku.com