Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, 2023.
“A ranar 17/08/2023 da misalin karfe 1100 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton cewa wani matashi dan shekara 35 mai suna Samaila Ilu da ke kauyen Dungun Tantama a karamar hukumar Hausa, ya bar gidansa a ranar 16/08/2023 zuwa wani wuri da ba a san inda ya nufa ba. PPRO ya bayyana.
Shiisu ya bayyana cewa an gano gawar Samaila a rataye a jikin bishiya da igiya.
Tawagar jami’an ‘yan sanda ta dauki gawar tare da kai ta asibiti domin tantancewa.
Kakakin ya kara da cewa daga baya an mika gawar ga 'yan uwansa domin yi musu jana'iza.
Published by isyaku.com