Zakuna sun cinye wani mutum mai shekaru 30 da haifuwa a dajin Dinokeng da ke Gauteng a Afirka ta Kudu.
Marigayin, mai suna Johannes Matshe, wanda ma’aikaci ne na daya daga cikin masu mallakar filayen a wurin ajiyar, Zakuna sun kashe shi ne a daren Lahadi, 13 ga watan Agusta, kuma an gano gawarsa a safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2023.
Kakakin hukumar, Hartogh Streicher, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta.
Published by isyaku.com