Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin raba wa kowacce jiha ciki harda babban birnin tarayya Abuja, tallafin naira biliyan 5, domin rage radadin cire tallafin man fetur, jaridar The Cable ta rahoto.
Gwamnati tarayya za ta warewa kowacce jiha biliyan 5 na cire tallafin mai
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ne ya bayar da sanarwar a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, lokacin da ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar tattalin arziki na kasa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci zaman majalisar tattalin arzikin kasar. Legit.ng ya wallafa.
Tun farko dai Legit.ng ta tattaro wasu batutuwa da za a tattauna a wajen taron NEC na yau, ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi halin da lalitar Gwamnatin Tarayya ke ciki da kuma sauran ƙarin matsalolin da suka shafi ƙasa.
Sai dai abu mafi muhimmanci da majalisar tattalin arziƙin za ta tattauna akai shi ne yadda za a gabatar da rabon kayan tallafi da za a bai wa 'yan Najeriya.
Za a ba da kayayyakin tallafin ne saboda ragewa 'yan ƙasa raɗaɗin da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya jefa su a ciki.
Majalisar ta kunshi gwamnonin jihohi 36, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da sauran jami'an gwamnati, rahoton Punch.
Published by isyaku.com