Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga kan kujerarsa.
Shugaban jam'iyyar na APC ya yanke shawarar ne a bainar jama'a ba tare da bayyana wani dalili ba. Legit ya wallafa.
Ya sanar da murabus dinsa bayan wata ganawa da kwamitin aiki na jam'iyyar a jihar a sakatariyar APC da ke garin Minna, a gaban babban mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Mohammed Nma Kolo, TVC News ta rahoto.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Jikantoro ya kuma sanar da mataimakin shugaban jam'iyyar a Neja ta arewa, Alhaji Aminu Bobi, a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar.
Ya kuma nuna yakinin cewa ficewarsa zai kawo ci gaba ga jam'iyyar a jihar, rahoton Daily Trust.
Jikantoro ya ce:
"Ina ganin ya zama dole kuma ya zama wajibi a gare ni na kira taron gaggawa don yi wa shugabannin jam'iyyar a jihar bayani, da kuma abin da ya faru jiya (Alhamis, 3 ga watan Agusta).
Abu na daya kenan; wanda na yi. "Abu na biyu, Ni, a nawa karan kaina, na yi muradin yin murabus daga mukamina, a matsayin shugaban jam'iyyar APC a jihar Neja.
"Wannan ne dalilin da yasa na yanke shwarar gayyata kafofin watsa labarai da su zo su nadi wannan taron."
Published by isyaku.com