Bayanai kai tsaye kan juyin mulkin Nijar: Tinubu na yunkurin tura sojoji


A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar yayin da sojoji masu tsaron shugaban kasa suka tsare Shugaba Mohamed Bazoum. Legit ya wallafa.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, karkashin jagorancin Shugaban Bola Tinubu na Najeriya, ta sanar da takunkumi daban-daban ciki har da yiwuwar tura sojoji idan shugabannin sojojin juyin mulki ba su sauka daga mulki ba.

Juyin Mulkin Nijar: Shugabanin sojoji na ECOWAS sun yi taro a Abuja


Shugabannin rundunar sojoji na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma sunyi taron gaggawa a Abuja yayin da sojoji suka karbi mulki a Nijar.

Shugabannin sojojin wadanda suka hadu a hedkwatar tsaro a Abuja a ranar Juma'a, 4 ga watan Agusta suna kira ga wadanda suka yi juyin mulkin su rungumi zaman lafiya kuma su saki tsararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN