Da bala’i ya shafi Najeriya idan ba mu karbi mulki ba – Cewar shugaban juyin mulkin Nijar


Janar Abdourahmane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar da ya karbi mulkin Nijar, ya yi ikirarin cewa sojoji sun karbe mulkin kasarsa ne domin ceto Najeriya daga bala'in da ke shirin faruwa da ita.


 Malaman addinin Musulunci da suka gana da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja ranar Juma’a sun gana da Tchiani a ranar Asabar 12 ga watan Agusta domin tattaunawa a Yamai.


 A cewar Sheik Bala Lau, Shugaban Jam’atul Izalatu Bida Waikamatu Sunnah, Tchiani ya yi ikirarin cewa juyin mulkin an yi da kyakkyawar niyya sosai, inda ya kara da cewa “sun yi kokarin kashe wata barazana da ke tafe da ba jamhuriyar Nijar kadai ba har ma da Najeriya za ta shafa.”


 Ba a san abin da Tchiani ke nufi ba saboda sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba.


 Amma ikirarin nasa ya zo ne bayan hedkwatar tsaron Najeriya ta ce wasu mutane na ingiza sojoji su karbe mulki a Najeriya.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN