Yanzu-Yanzu: Shugaban Juyin Mulkin Nijar Ya Amince Da Tattaunawa Da ECOWAS, Bayanai Sun Fito


Shugaban juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya amince ya hau teburin sulhu da hukumar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS).

Janar Tchiani ya amince ya tattauna da ƙungiyar ECOWAS ne bayan ya gana da tawagar malaman addinin musulunci a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, a Jamhuriyar Nijar. Legit.ng ya wallafa.

A cewar rahoton Zagazola Makama, Firaministan Jamhuriyar Nijar shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Nan ba da jimawa ba za a hau teburin sulhu
iraministan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, Janar Tchiani ya bayar da ƙofar tattaunawa da ECOWAS, inda ya nuna fatansa cewa tattaunawar za ta wakana a cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

Mun amince sannan shugaban ƙasar mu ya bayar da kafar da za a hau teburin sulhu. Yanzu za su koma su gaya wa shugaban ƙasar Najeriya cewa sun ji daga gare mu... Muna fatan cewa a cikin ƴan kwanaki masu zuwa, wakilan ECOWAS za su zo nan su same mu domin tattauna yadda za a janye takunkumin da aka ƙaƙaba mana." A cewarsa.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN