Illustrative picture |
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani mai suna Friday Igberase, bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai suna Cathrina Ouke ‘yar shekara 60 fyade.
An tattaro cewa wanda ake zargin mai shekaru 52 da haihuwa ya yi wa tsohuwar fyade ne a gonarta da ke Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Dankwara, ya ce rundunar ‘yan sandan reshen Uromi ta jihar ce ta kama wanda ake zargin.
CP ya ce sashin ya samu korafi daga wanda aka cutar cewa a watan Yuli, wanda ake zargin mai shekaru 52 ya kai mata hari a gonarta, ya yi mata fyade tare da yi mata barazanar kashe ta idan ta fada wa kowa.
"Matar da aka yiwa fyaden ta kuma yi zargin cewa tun da aka yi mata fyaden tana fama da wani bakon cuta."
Shugaban ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan sun kai wanda aka cutar zuwa asibiti domin yi mata magani sannan kuma sun kama wanda ake zargin wanda ya amsa laifinsa.
Ya ce an mayar da shari’ar zuwa sashin kula da jinsi na sashen binciken manyan laifuka na jihar (CIB) a birnin Benin.
Published by isyaku.com