Yadda matashin dan sanda ya barke da kuka bayan an kore shi daga aiki aka tube masa tufafin Yan sanda - Bidiyo


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ta gurfanar da wasu ‘yan sanda biyu Insp Ahmed Suleiman da  PC Mahmood Muhammed wanda ke aiki a hedikwatar ‘yan sanda na Dumne, a gaban Kotun cikin gida na Yan sanda.


 An yi wa mutanen shari'a akan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da rashin cin amana da bata suna darashin Halaye na gari, Kisan kai da, da aiwatar da Hukunce-hukuncen da ba bisa ka'ida ba sabanin sakin layi na 'E'(I)(iii) da 'Q'(I) (iii) na Jadawalin Farko.  na Dokar 'Yan Sanda da Dokokin, Sashe na 370, 2020 kamar yadda aka gyara.  Rundunar ta same su da laifi kamar yadda aka tuhume su kuma ta ba da shawarar a hukunta su ta hanyar kora daga aiki.  Za a gurfanar da dukkansu a gahan kotu tare da sauran wadanda ake zargin.



 An cire kayan aikin Constable yayin da za a cire na sufeto bayan ya cika wasu ka"idodin gudanarwa.



 Kwamishinan ‘yan sanda CP Afolabi Babatola ya gargadi jami’an rundunar da su kasance tukuru a kan lokacin aiki tare da nisantar duk wasu laifuffukan da suka shafi ladabtarwa.



 Kalli bidiyon Mahmood Muhammed yana kuka yayin da ake cire masa kayan aikin Yan sanda a kasa

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN