A cikin jerin sakonnin text ga wani abokinsa da aka ruwaito CNN ta gani, Bazoum ya ce "an hana shi hulda da mutane" tun daga ranar Juma'a, Kuma aka hana ba shi abinci ko magani.
Bazoum ya ce ya shafe mako guda yana rayuwa babu wutar lantarki, lamarin da ya zama ruwan dare ga daukacin 'yan Nijar bayan da Najeriya ta katse wutar lantarki sakamakon juyin mulkin.
Bazoum ya ce duk abincin da aka kawo masa ya lalace, kuma yanzu yana cin busasshiyar taliya da shinkafa.
Ko da yake masu juyin mulki sun ki tattaunawa da mukaddashin sakatariyar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland a ziyarar da ta kai Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, duk da haja Bazoum na tuntubar wasu kasashen waje.
Published by isyaku.com