Yanzu-Yanzu: Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar APC Kan Jagororin Majalisa


Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta nesanta kanta daga jagororin majalisa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas suka sanar.

Shugabannin majalisar dai sun sanar da sabbin jagororin majalisar ne a zaman da aka gudanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli. Legit Hausa ya wallafa.

Amma da yake jawabi ga gwamnonin jam'iyyar, Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar na ƙasa, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da hannu a cikin sunayen ƴan majalisar da aka sanar, cewar rahoton Daily Trust.

Adamu ya ce shi ma sai dai ya ji raɗe-raɗi na yawo a kafafen watsa labarai cewa an naɗa jagororin majalisar.

Adamu bai san da cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba

Shugaban jam'iyyar ya ce duk da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar lokacin da suka kai masa ziyara barka da Sallah a ƙarshen mako, bai san cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba.

A kalamansa:

"Amma yanzu kawai na ke ji a matsayin jita-jita a kafafen watsa labarai cewa an fitar da wasu sanarwowi a majalisar dattawa da ta wakilai."

"Hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) bai fitar da wannan bayanin ba ko sanar da zaɓin jagororin ba."

"Sannan har sai mun tattauna a tsakaninmu mun fitar sannan mu tura musu a rubuce wanda hakan shi ne abinda aka saba yi, ba mu da niyyar kaucewa daga wannan tsarin."

"Domin haka kowace irin sanarwa da shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, kakakin majalisar wakilai ko mataimakinsa suka yi, ba daga gare mu bane."

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN