Daga karshe sabbin shugabannin Majalisar Dattijai sun bayyana


Bayan shafe lokaci ana dambarawar siyasa a Majalisar wakilan Najeriya, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da waɗanda suka samu nasarar zama jagororin majalisar dattawa ta 10
.

Channels tv ta tattaro cewa Sanata Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi sabbin shugabannin ne ta hanyar maslaha. Legit ya wallafa.

Jagororin bangaren masu rinjaye
Sabbin jagororin majalisar sun haɗa da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Dave Umahi daga Ebonyi a matsayin mataimakinsa.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya zama babban mai ladaftarwa na majalisa yayin da Sanata Lola Ashiru, ya samu nasarar zama mataimakinsa.

Sabbin jagororin majalisar dattawa daga ɓangaren marasa rinjaye
A ɗaya bangaren kuma Sanata Akpabio ya bayyana sabbin shugabanni daga ɓangaren marasa rinjaye.

Sun ƙunshi Sanata Simon Davou (Filato ta arewa – PDP) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye yayin da Oyewunmi Olarere (Osun ta yamma – PDP) ya zama mataimakinsa.

Sauran sun haɗa da Sanata Darlington Nwokeocha mai wakiltar jihar Abia ta tsakiya a inuwar LP a matsayin mai ladaftarwan marasa rinjaye da kuma Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya) a matsayin mataimakinsa.

Idan baku manta ba 'yan takarar da jam'iyyar APC ta marawa baya ne suka samu nasarar zama shugabannin majalisar tarayya ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni, 2023.

Godswill Akpabio ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa yayin da Honorabul Tajudeen Abbas ya zama sabon kakakin majalisar wakilan tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN