Ya isheka: Tsohon Gwamnan PDP ya gargadi Gwamnan APC kan magana a midiya


Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya shawarci magajinsa, Rev. Fr.  Hyacinth Alia ya dena yi masa shari'a da yanke hukunci a kafafen yada labarai yana mai gargadin cewa shi mutum ne kuma akwai iyaka da zai iya jurewa irin wadannan hare-hare.

 Tsohon Gwamnan ya shawarci Gwamna Alia da ya mai da hankali kan aikin gwamnati da kuma cika alkawarin da ya yi wa jama’a maimakon bata sunansa. Vanguard ta rahoto.

 Tsohon Gwamnan wanda ya ba da wannan shawarar a ranar Talata cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Terver Akase ya fitar, ya yi nuni da cewa “Harin na baya-bayan nan da Gwamnan ya kai wa Cif Ortom na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai inda ya caccaki magajinsa kan batutuwa da dama.  , yana bayyana shi a matsayin wanda bai yi wa jama’a komai ba cikin shekaru takwas.”

 Sanarwar ta kara da cewa, “Hare-haren da ba a san ko su wanene ba sun zama abin takaici.  Da ma mun mayar da martani daidai gwargwado, amma mun gwammace mu shawarci Gwamna da mukarrabansa da su maida hankali wajen samar da ci gaba ga al’umma.  Shi ma tsohon Gwamnan mutum ne, kuma akwai iyaka da zai iya jure wa cin zarafin da kafafen yada labarai ke yi masa.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN