Daga karshe dai hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) a gaban kotu.
Emefiele yana tsare tun lokacin da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi a watan jiya. Hukumar DSS dai ta kama Emefiele a gidansa da ke Legas inda ta dauke shi a cikin wani jirgin sama na sirri zuwa Abuja. A safiyar Talata, 25 ga watan Yuli, an gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas.
Kalli bidiyo a kasa
Published by isyaku.com