Wani lamari mai ban mamaki ya faru a babbar kotun tarayya da ke Legas inda aka gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da aka dakatar a safiyar yau.
Ku tuna cewa a yau ne hukumar DSS ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya bisa laifin mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba amma an bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 20 tare da mutum daya.
Vanguard ta ruwaito cewa jim kadan bayan bayar da belin, an samu hatsaniya tsakanin jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da jami’an hukumar gyara hali ta kasa (NCS) kan wanda zai tafi da wanda ake tuhuma.
An kuma tattaro cewa a halin yanzu an ajiye motoci kirar Hilux guda biyu na hukumomin gwamnati biyu a kusa da kofar shiga kotun.
Published by isyaku.com