Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan sanda sun kama wasu mutane hudu da suka yi yunkurin kai masa hari a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun bayyana wa ‘yan sanda wani gagarumin shiri na tayar da bama-bamai a babban masallacin Modibbo Adama, gidan Atiku, da kuma jami’ar Amurka da ke Yola.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Paul Ibe ya fitar, Atiku ya ce.
“Muna sanar da al’ummar Najeriya cewa da misalin karfe 9:44 na daren Lahadi, 23 ga Yuli, 2023, an kama wani mai neman tabbatar da gidan mai girma Atiku Abubakar a Yola a kofar gidan.
“Mutumin wanda jami’an tsaro suka kama shi a gidan Atiku Abubakar, daga baya aka mika shi ga ‘yan sanda, bayan da ‘yan sandan suka ci gaba da yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana sunan sa a matsayin Jubrila Mohammed mai shekaru 29 kuma ya bayyana cewa shi dan Boko Haram ne daga Damboa a jihar Borno.
“Wanda ake zargin ya kuma sanar da ‘yan sanda cewa shi da abokan aikinsa, wadanda aka kama, su ma sun yi niyyar kai hari kan kungiyoyi masu alaka da Atiku Abubakar da wasu wurare masu muhimmanci a Yola.
Muna yaba wa ‘yan sanda bisa aikin da suke ci gaba da yi a wannan bincike na musamman. Muna kuma rokon sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa su ci gaba da kasancewa a kan bayanansu.”
Published by isyaku.com