Da dumi-dumi: Yan daba sun kashe dan sanda a jihar Kano


An halaka wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira a unguwar Yakasai cikin Kano Municipal a yammacin ranar Talata.

Shaidun gani da ido sun gayawa jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku ne lokacin da wasu ƴan daba suka kai wa wani da ake zargin ɗan daba ne hari bayan ya sauko daga Keke Napep a wajen asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad. Legit Hausa ya wallafa.

Shaidar ganau ɗin wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa mutumin yana saukowa daga Keke Napep ɗin suka farmasa da hari.

A kalamansa:

Lamarin ya fara ne lokacin da mutumin ya sauko daga Keke Napep, nan da nan wasu ƴan daba suka farmasa da makamai."
"An ɗauki lokaci kafin zuwan ƴan sanda waɗanda suka kasa korarsu. Ƴan daban sun koma kan ƴan sanda inda suka fara jifarsu da duwatsu."

"Lokacin da ƴan sandan suka yi ƙoƙarin kaucewa harin da gudun a yi musu ɓarna ne ɗan sandan ya faɗo nan da nan suka yi kansa inda suka yanka shi har lahira."
Ya ƙara da cewa a cikin ƴan kwanakin nan, ƴan daba masu gaba da juna sun sha ba hammata iska a unguwar, cewar rahoton Platinum Post.

Ƴan sanda na gudanar da bincike kan lamarin

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, kan lamarin ya bayyana cewa rundunar ba ta samu wani bayani ba amma ana gudanar da bincike.

"Ba mu samu wani bayani ba irin wannan amma muna bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abinda ya faru." A cewarsa.
'Yan Daba Sun Halaka Wani Dan Kasuwa a Kano

A wani labarin na daban kuma, ƴan daba sun halaka wani ɗan kasuwa har lahira a jihar Kano ta hanyar caccaka masa wuƙa.

Ƴan daban dai sun halaka ɗan kasuwan ne mai suna, Alhaji Auwalu Gambo a gidansa da ke a ƙauyen Dakasoye cikin ƙaramar hukumar Garun Malam ta jihar

Published by isyaku.com

2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. SHIKENAN DARA TA CI GIDA KUMA A CIKIN GIDA

    ReplyDelete
  2. Wallahi dole a day mataki yanzu abin ya wuce lissafin yaro

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN