Wata mata yar shekara 50 ta lakada wa mahaifiyarta mai shekara 75 dukan tsiya, duba dalili


Ƴan sanda a jihar Anambra sun cafke wata mata mai suna Ukamaka Udugbo mai shekara 50 a duniya bisa lakaɗawa mahaifiyarta mai shekara 75 duka a yankin Abagana na ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar.

Matar dai an ɗauke ta ne a cikin wani faifan bidiyo tana cin zarafin mahaifiyarta ta hanyar lakaɗa mata duka, cewar rahoton PM News.

DPO na ofishin ƴan sandan Abagana, SP Ifeanyi Umeh shi ne ya tabbatar da cafke matar da lokacin da wata ƙungiya mai zaman kanta '50-50 Action Group of the WomenAid Collective' (WACOL) ta ziyarce shi kan lamarin. Legit ya wallafa.

Umeh ya bayyana cewa sun samu labarin yadda matar ta ci zarafin mahaifiyarta mai suna Theresa Nwaokaka, wanda hakan ya sanya suka yi gaggawar zuwa cafko ta.

Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincikensu za su tura da lamarin zuwa hedikwatar ƴan sanda ta birnin Awka.

An yi Allah wadai da halin matar
Ify Unachukwu, shugabar tawagar ta nuna godiyarta ga ƴan sanda kan yadda suka tunkari lamarin da gaggawa inda ta buƙaci da su tabbatar an ba lamarin muhimmanci domin hakan ya zama darasi ga saura.

Unachukwu ta bayyana lamarin a matsayin abun takaici ƴa ta lallasa dattijuwar mahaifiyarta inda ta yi kira ga matasa da su kiyayi yin koyi da wannan mummunar ɗabi'ar, rahoton The Punch ya tabbatar.

A cikin bidiyon an nuna Udugbo na lakaɗawa dattijuwar mahaifiyarra duka yayin da ta ke mata wanka a ƙauyen Obeagu Umudun cikin yankin Abagana.

Nwaokaka tana rayuwa ne a gidan ɗiyarta inda ta ke kula da ita.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN