Shugaban kasa Bola Tinubu ya sa dokar ta baci kan abinci da ruwan sha don taimakawa rage radadin cire tallafin Mai don haka za a ba mutane milyan 15 tallafin dubu takwas cikin kusan milyan 150 da aka ce sun abka a mummunan talauci.
Ga abinci ba kudin Saya mutane masu kudi suna bin kasuwanni suna sayan gero da dawa da shinkafa da masara da wake suna loda manyan motoci suna kaiwa kudu da wajen kasa. Alamu sun nuna yunwa za ta yi barna idan gwamnati ta doge kan cire tallafin Mai.
Ina dalilin da ita gwamnati ba za ta gyara matatun manta ta rika tacewa ba don farashin ya sauka. Gwamnati ta gwammace yan Nigeria su mutu da yunwa kenan saboda wasu tsirarin da ke amfana da tallafin mai shin sun fi karfin gwamnati ne.
Me yasa gwamnati baza ta rike tallafin ba ita ta ci moriyarsa ta taimaki mutanen ta. Shin lokacin shugaban kasa Yar Adua babu tallafin ne ya rage farashin mai. Idan sun dage kan wannan raayi su sani Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi suna gani kujerar mulki zata musu zafi.
Komai zai iya faruwa saboda matsalar mai kadai ta lalata kowace hidimar rayuwa don son zuciyar mutane kalilan. Mutane ba za su zauna suna kallo yunwa ta kashe su ba a kasa mai arzikin manfetir ta farko a Afirka cikin kungiyar OPEC.
Mu ci gaba da adduah Allah ya kawo mafita a ruwan sanyi. 08062333065
Daga Muazu Hardawa Bauchi.
Published by isyaku.com