Tinubu Ya Aikawa EFCC da DSS Sunayen Waɗanda Za Su Zama Ministoci


Yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe kwanaki 40 a ofis, jama’a sun kai bango wajen sauraron wadanda za a zaba su zama Ministoci.

A rahoton da Punch ta fitar a ranar Litinin, an samu labari ‘yan majalisa sun fara damuwa kan abin da ya hana aiko sunayen wadanda za a ba Minista. Legit Hausa ya wallafa.

Wasu Sanatoci da su ka yi magana ba tare da bari an kama sunayensu ba, sun ce ba su tunanin za a cigaba da bata lokaci kafin a fitar da Ministocin kasar.

Sunayen ya kai teburin EFCC da DSS


Majiya ta shaidawa jaridar cewa jami’an EFCC da DSS da sauran hukumomin tsaro su na daf da kammala binciken wadanda ake sa ran su rike mukamin.

Hukumar DSS ta fararen kaya da na hannun-daman shugaban kasan su na tantance wadanda aka zaba kafin a fitar da sunayensu zuwa ga majalisar dokoki.

Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Alex Egbona ya ce dole ne a sanar da Ministoci cikin watanni biyu, ya na sa ran ba zai wuce makon yau zuwa gobe be.

Shawarwarin da ake ba Gwamnati


‘Dan majalisar Ideato, Hon, Ugochinyere Ikenga ya ce an kusa sanar da sababbin Ministoci.

Akwai irinsu Uche Nwosu da ke ganin babu laifi a dauko ‘Yan Najeriya da ke kasashen waje a ba su kujerar domin nemo wadanda su ka san kan aiki.

Hadimin Atiku Abubakar, Demola Olarewaju ya ce shugaban kasan ba zai iya dauko wadanda su ka san aiki ba, domin dole ya yi wa ‘yan siyasa sakayya.

Ita kuwa wakiliyar mata a kungiyar ECOWAS, Beatrice Eyong ta na so shugaba Bola Tinubu ya warewa mata 50% na duk mukaman da zai raba a mulkinsa.

Idan an tashi rabon mukaman, jaridar Tribune ta ce majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta ware ko da 10% na mukamai domin masu nakasa.

Ana rade-radin cewa a gwamnatin nan, masu ba shugaban kasa shawara za su samu karfi sosai.

Ayodele Fayose zai zama Minista?

A rahoton da mu ka fitar a farkon makon nan, an ji Ayodele Fayose ya fadi dalilinsa na marawa Bola Tinubu baya kan PDP, kuma ya ce ba ya neman Minista.

Fayose yake cewa duk wanda ya kai shekara 65 a Duniya, kamata ya yi Bola Tinubu ya fada masa ya kawo ‘ya ‘yansa a ba shi mukami, domin shi ya tsufa.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN