Labarin soyayya tsakanin ɗan Indiya da ƴar Pakistan ya ƙare a kurkuku


Labarin soyayya tsakanin wata 'yar Pakistan da wani Ba'indiye wanda suka hadu a dandalin wani shahararren wasan intanet da ake kira PUBG ya ɗauke hankalin mutane da dama a indiya bayan mosyna biyu sun ƙare a gidan yari.

Seema Ghulam Haider, mai shekaru 27 da haihuwa , ta haɗu da Sachin Meena ɗan shekara 22, ta hanyar dandalin wasan shekaru biyu da suka wuce kuma kwanan nan ta tafi Indiya don ta zauna tare da shi.

Ta shiga Indiya ba bisa ka'ida ba a watan Mayu tare da ƙananan 'ya'yanta hudu kuma suna zaune tare da Mista Meena a garin Greater Noida - wani birni a arewacin jihar Uttar Pradesh - na tsawon wata guda, in ji 'yan sanda.

A ranar Talatar da ta gabata aka kama masoyan. Kotu ta daure su a gidan yari na tsawon kwanaki 14. Yaran matar suna tare da mahaifiyarsu. Ma’auratan sun shaida wa manema labarai cewa suna son su yi aure kuma su zauna tare. 'Yan sanda sun ce suna gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Labarin soyayyar ta Indiya da Pakistan ya haifar da mahawara kan rawar da duniyar yanan gizo ke takawa wajen haɓaka alaƙar rayuwa ta zahiri da kan ƙetara iyakokin ƙasa.

Soyayya ta kankama a dandalin PUBG


Seema ta auri Ghulam Haider, mazaunin lardin Sindh na Pakistan, a watan Fabrairun shekarar 2014. Ma'auratan sun haifi 'ya'ya hudu - mata uku da namiji daya.

Bayan shekaru biyar da aurensu, mijinta ya koma Saudiyya da aiki, sai Ms Haider ta fara buga wasan PUBG don ta shagaltar da kanta.

"Na kasance ina buga PUBG tsawon sa'o'i biyu zuwa uku a rana kuma ta haka ne na fara sanin Sachin," kamar yadda ta shaida wa BBC Hindi, ta ce sun yi musayar lambobin waya suka fara magana akai-akai.

B

ayan dangantakarsu ta ci gaba da bunƙasa sama da shekaru uku, Ms Haider ta yanke shawarar ƙaura zuwa Indiya don auren Mista Meena.

Ta zargi mijinta da yi mata dukan tsiya, kuma ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta sake shi. Mista Haider ya musanta zarge-zargen rikicin cikin gida da kuma kisan aure.

Ya zargi Ms Haider da sayar da gidansu a Pakistan da kuma gudu da 'ya'yansu da kayan yari.

Yadda masoyan suka haɗu


'Yan sanda sun ce Ms Haider da Mista Meena sun fara haɗuwa ne a ƙasar Nepal a watan Maris kuma sun zauna a wani otal na kwanaki biyu kafin suka koma kasashensu.

Babban jami'in 'yan sanda a Greater Noida Saad Miya Khan ya shaida wa BBC cewa a watan Mayu, Ms Haider ta sake tafiya zuwa Nepal da 'ya'yanta hudu bisa takardar izinin yawon buɗe ido. Daga nan ta hau motar bas zuwa Delhi.

‘Yan sandan sun ce ta shaida musu cewa ba ta sayar da gidan mijinta ba amma wani fili ne na iyayenta don tara kuɗin tafiyar kuma ta samu ra’ayin shiga Indiya ta Nepal ne daga wani bidiyo da ta gani a YouTube.

Mista Meena, wanda ke zaune a garin Rabupura a yankin Greater Noida kuma yana aiki a wani kantin kayan abinci, ya yi hayar ɗaki don ya zauna da Ms Haider da 'ya'yanta.

Wanda ya ba shi hayar ɗakin, Girish Kumar, ya shaida wa BBC cewa bai taɓa zargin wani abu da ya saɓa doka ba, domin Mista Meena ya gabatar da duka takardun gwamnatin da ake bukata yayin da ya ke karɓan hayar ɗakin, kuma iyayensa ma sun zo sun ziyarci masoyan.


Wanda ya ba mosoyan hayar ɗaki, Girish Kumar, ya ce bai taɓa zargin wani abu da ya saɓa doka na gudana ba.


Yadda aka damke su


Rahotanni sun ce masoyan sun gana da wani lauya na yankin don neman shawara game da zaman Ms Haider a Indiya a makon da ya gabata amma lauyan ya kai ƙaransu wurin 'yan sanda, jaridar Times of India ta ruwaito.

Lauyan ya shaida wa jaridar cewa, "Na firgita lokacin da na gano cewa ita da 'ya'yanta na dauke da fasfo din Pakistan," in ji lauyan, ya kuma ƙara da cewa Ms Haider na gudanar da bincike kan yadda za a yi aure a Indiya.

Lauyan ya yi ikirarin cewa Ms Haider ta ce mijinta (Ghulam Haider) ya kan yi mata fyaɗe kuma ta yi shekaru hudu ba ta haɗu da shi ba.

Ya kuma ƙara da cewa Ms Haider ta tashi ta tafi da aka tambaye ta batun bizarta ta Indiya, sai wani abokinsa ya bi ta.

"Lokacin da na sami labarin cewa suna zaune a Rabupura, na sanar da 'yan sanda," in ji lauyan.

Tare da masoyan biyu, 'yan sanda sun kama mahaifin Mista Meena kan laifin bai wa Ms Haider mafaka ba tare da biza ba.

Masoyan sun roƙi gwamnatin Indiya da ta taimaka musu su yi aure.

Shi kuma mijin Ms Haider, ya yi ikirarin cewa an “yuadari” matarsa ​​ta hanyar anfani da dandalin PUBG kuma yana son a mayar da ita Pakistan tare da ‘ya’yansu.

Rahotun shafin BBC Hausa

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN