Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zama shugaban ƙungiyar Economic Community of West African States (Ecowas) ta ƙasashen Afirka ta Yamma. BBC Hausa ya wallafa.
Tinubu ya maye gurbin Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau yayin taron da ƙasarsa ke karɓar baƙunci a yau Lahadi karo na 63.
"Za mu ɗauki dimokuraɗiyya da muhimmanci. Tana da wuya amma ita ce tsarin gwamnati mafi dacewa," a cewar Tinubu bayan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar.
Wannan ne taro na biyu da shugaban na Najeriya ke halarta a ƙasashen waje tun bayan da ya hau mulki a watan Mayu biyo bayan nasarar da ya yi a zaɓen watan Fabrairu.
Baya ga alwashin jagoranci na gari da ya ci, Tinubu ya bayyana damuwa kan yadda "matsalar tsaro da ta'addanci ke mayar da yankin Afirka ta Yamma baya".
Published by isyaku.com